XtGem Forum catalog
Sulaiman20Ibn20Hujjah 2
Barka20Da20Zuwa
Shafi20Mai20Albarka



¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶

Zaka iya kiran wayata tanan
HomeBlogAbout MeBayani Akan AZUMIAikin Hajji da UmaraMa anar Shi aAbin da Aka HanaSamun FalalaKasuwanci Mai RibaMahimmancin Addu o iBayanin ZakkaSALLAMATA A MUSULUNCITSARKITAUHEEDI DA AQIDAAYYUKAN ZUCIYAMAHIMMANCIN DA AWATAMBAYA DA AMSASheikh jafar mahmud AdamWadansu websides


SHIGA NAN DOMIN SAMUN KARATUTTUKAN MALUMAN SUNNAH


Sheik Lawan Abubakar Gadon Kaya tafseer2017



02/05/24
FB Pantami


Ibn20Hujjah
Source: Google news
0Mozilla/5.0




SULAIMAN Ibn Hujjah

* No categories

Online: Guests: 1


Sulaiman20 FaceBook


BAYANI AKAN SALLA

Kiran salla da kuma yin ikama ga maza mazauna gida wani yana dauke ma wani, kuma sunna ce ga mutun daya ko matafiyi amma kuma an kyamace shi ga mata, kuma kiran salla bai inganta har sai lokaci yayi sai dai sallar asuba. ita kam ya inganta a kiran fari bayan rabin dare ya wuce.
**SHARUDAN SALLA**
(1) Musulunci
(2) Hankali
(3) Tasawa fahimtar ina aka sa gaba (ba dole sai ya balaga ba)
(4) Tsarki da samun iko
(5) Shigar lokaci.
Lokacin sallar azuhur daga gushewar rana daga tsakiyar sama zuwa har inda inuwar abu zata yi dai-dai da tsawonsa,
Sannan Kuma lokacin sallar la'asar zababbe shine inda duk wani abu zai yi dai-dai da tsawonsa sau biyu. sai kuma lokacin larurunsa shine zuwa faduwar rana.
Sannan lokacin magriba yana biye har sai jan rana ko fatsi-fatsin ta ya bace.
Sai kuma lokacin sallar isha'i shine zababben lokacin ta har rabin dare daga nan kuma har zuwa alfijir ya fito lokacin ta ne na larura sanman kuma a lokacin sallar asuba har zuwa fitowar rana.


(6) Suturce al'aura ta fara da samun ikon yin haka din da wani abu wanda bai nuna fatar jikin mutum; amma al'amuran mutum namiji balagagge ga nuni da a ka yi shi ne daga cibiyarsa zuwa gwiwar samunsa, amma mace 'ya cikikiya ba (baiwa ba ita duk jikin ta al'aura ne a cikin salla amma ban da fuskar ta.
(7) Nisantar kazanta (najasa) a jikinsa, wurin sallansa matukar an samu ikon yin haka din.
(8) Fuskantar alkibla tare da matukar ana da ikon yin hakan.
(9) Niyya.


**RUKUNNAN SALLA**

*Rukunan Salla guda goma sha hudu ne*
(1) Tsayuwa tare da ikon haka din a cikin sallan farilla.
(2) Kabbarar harama
(3) Karatun fatiha
(4) Yin ruku'i cikin kowace raka'a
(5) Dagowa daga ruku'i.
(6) Daidaituwa a tsaye bayan dagowa daga ruku'i.
(7) Yin sujada a kan gabbai bakwai
(8) Zama tsakankanin sujaddi biyu.
(9) Karatun tahiya ta karshe.
(10) Zama don tahiya.
(11) Yin salati ga annabi (s a w) a tahiyar karshe.
(12) Sallama ta farko.
(13) Nutsuwa a cikin rukunan aikin salla.
(14) Jerantawar wadannan rukunnan.
Kaga wadannan rukunan salla ba ta inganta sai da su, kuma ta na baci da barin dayan wadannan rukunnan da mantuwa aka bari ko kuwa da gangan ne aka bari.


**WAJIBAN SALLA GUDA TAKWAS NE**

(1) Dukkan kabbarorin in ban da kabbarar harama wajibi ne.
(2) Fadar sami Allah liman hamida hu (Allah ya na jin mai gode masa).
(3) Da kuma (rabbana wa lakal hamdu) Ubangijinmu gareka godiya take, lokacin dagowa daga ruku'i.
(4) Fadar (subhana rabbiyal azim) tsarki ya tabbata ga Ubangijina mai girma, a cikin ruku'i sau daya.
(5) Fadar (subhana rabbiyal a'ala) Tsarki ya tabbata ga ubangijina mafi daukaka sau daya cikin sujjada.
(6) Fadar (rabbig firni) Ya Allah ka gafartamin, tsakanin sujjada biyu.
(7) Karatun tahiya ta farko.
(8) Zama domin wannan tahiyar.
Wadannan wajibin in mutum ya bar su da gangan sallar sa ta baci; in kuwa da mantuwa ne to sai yayi sujuda ta rafkanuwa don gyaran sallar.


**AMMA SUNNONIN SALLA**
Su ne zantutuka da kuma ayyuka, kuma salla bata baci don barin wani abu daga cikinsu koda da gangan ne.
* To sunnonin zantuka:- addu'ar budewar ko farawar salla, neman tsari da yin basmala da fadar amin da bayyanata wurin bayyanawar, da karatun abin da ya saukaka daga ayoyin Al'kur'ani amma shi mamu (watau mabiyi an hana shi ya bayyana nasa karatun amma wanda ke yi shi kadai am bashi zabi) da fadin hamdan kasiran diyyiban mubarakan fihi mil'as samawati wal ardi....(godiya mai yawa kyakyawa masu albarka a cikinsa; cike da sammai da kuma cikin kasa...(da sauransu) godiya da kuma duk abin da aka yi tasbihi na ruku'i da sujjada da kuma ya Allah ya gafarta mana, yin addu'a kafin sallama (duk sunna ne na magana cikin salla).


**SUNNONIN AYYUKA A SALLA**
Daukaka hannaye biyu tare da kabbarar harama lokacin ruku'i da kuma lokacin dagowa daga ruku'in da kuma lokacin dagowa daga tahiya ta farko, da kuma dora hannun dama akan na hagu lokacin da yake tsaye, da kuma kallo inda zai sa goshinsa, da bude kafafuwansa ko duga dugansa lokacin tsayuwarsa, da fara aza gwiwowinsa sannan tafukansa sai goshi sai hancinsa lokacin sujjada; da kuma nesantar da damatsansa daga sassannin hakarkarinsa; da kuma bude cinyoyinsa daga barin junansu (waton kar ya hada su).
Ya kuma mike duga-dugainsa kuma ya rabe kar ya hade su wuri daya; kuma ya dora cikin 'yan yatsunsa akan kasa kuma ya dan dai daita hannayensa daura da kafadunsa yana hade 'yan yatsun hannayen akan doron kasa; kuma da tsayuwarsa a kan kafafuwansa ya kuma dogara da hannayensa kan gwiwowinsa; da kuma kan kafafuwansa ya kuma dogara da hannayensa kan gwiwowinsa da kuma kan duwawunsa tsakaninin sujjada biyu da kuma wajan tahiyar farko.


Amma a tahiya ta biyu zaman durkushe ne zai yi sai kuma ya dora hannayensa a kan cinyoyinsa yana mai shinfida su kuma yana mai motsawar 'yan yatsunsa a tsakanin sujada biyu, haka nan ma zai yi cikin tahiya.
Sai dai zai nade dan yatsansa kamar dai ta biyu da kuma ta tsakiya sai ya matse ta da babban dan yatsan kuma manuniya ya rika nunawa ko mike ta tana fuskantar alkibla lokacin ambaton Allah da yin addu'arsa; wannan nuni ya na nufin Allah shi kadai ne. sannan kuma juyawarsa dama da hagu domin yin sallama, kuma ya fara ta wajen dama.


**SUJJADAR RAFKANUWA**
An sunnanta idan mutum ya zo da magana ta shari'a a inda ba wurinta ba da mantuwa kamar karatun Alkur'ani lokacin sujjada; kuma ba komai a kansa.
kuma idan da zai bar sunna to an halatta masa ita (wato sujjadan kabli).
ta kan zama wajibi akansa idan ka yi karin ruku'i, sujjada, tsayuwa, zama yayin sallama, ko kuma ya yi wani kuskure wanda ya ke bata ma'anar kalma, ko ya bar wajibi, shakka (kokwanto) game da kari.
Idan lokacin aikata ta (ke nan sannan yayi sujjadar rafkannuwa).
Salla tana baci in aka bar sujjada ta rafkanwa wacce take ta wajibi.
In mutum ya yi shakka cikin sallarsa; to sai ya yi sujjadai biyu kafin sallama ko bayan sallamar. in har ya manta da sujjadar har lokaci yayi tsawo, to sujjadar ta fadi.